Kungiyar kwadagon najeriya (NLC) ta goyi bayan barazanar da kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasar (NUPENG) tayi na tsunduma yajin aikin gamagari akan zargin yin amfani da sojoji wajen korar ma’akata daga wurin hakar mai na Oritsetimeyin.
Sanarwar da shugaban nlc na kasa, Joe Ajaero, ya fitar a yau Juma’a tayi tir da allawadai da yin amfani da sojoji a kan ma’aikatan hakar man, inda ya jaddada goyon bayansa ga matakin na NUPENG.
NLC ta kuma yi barazanar zafafa martaninta a kan rikicin matukar aka ci gaba da saba yarjejeniya tare da yin amfani da sojoji da sauran hukumomin tsaro wajen yin katsalandan a kan harkokin kwadago.
Martanin Ajaero na zuwa ne sakamakon wata takaddama da ta ki ci taki cinyewa tsakanin mamallaka rijiyar mai ta Oritsetimeyin da NUPENG a kan zargin saba yarjejeniyar da bangarorin 2 suka kulla cikin aminci.
A farkon makon da muke ciki ne NUPENG ta shigar da korafi ga gwamnatin tarayya, tare da yin gargadin daukar mataki matukar aka yi amfani da sojoji ko wasu wajen korar mambobinta ko ma’aikatan wucin gadi, da kuma kin mutunta yarjejeniyar da bangarorin 2 suka kulla cikin aminci.
Sai dai, da safiyar jiya Alhamis, an yi zargin cewar an kai wata tawagar dakarun sojin ruwa ta jirgin sama zuwa rijiyar man ta oritsetimeyin domin su kori ma’aikatan.
Sakamakon al’amarin, NUPENG ta yi barazanar ayyana yajin aikin gamagari matukar gwamnati ta gaza takawa hukumar gudanarwar rijiyar man da hukumomin tsaro burki.
Dandalin Mu Tattauna