Kasashen sun hada da Jamhuriyar Nijar, Mali, Chadi, Maurtitania, Ivory Coast da kuma Burkina Faso.
A cewar Dr. Fatimatou Mousa, kwararriya a fannin tsarin iyali, ta ce wannan shiri zai taimaka wajen baiwa mata da yara kanana ‘yan cinsu a lokacin rayuwarsu.
“Wannan shiri zai baiwa mata damar biyan bukatunsu da samun ‘yan ci wanda hakan zai tamaka wajen samun biyan bukatun kansu.” In ji ta.
A shekarar 2013 da Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki moon, ya kai ziyara kasar Nijar ne, hukumomin kasar suka nemi a tallafa musu domin biyan wannan bukata in ji Ministar al’umar Nijar, Madame Mai Chibi Kadijatou Dandobe.
“Yaro ya kamata a bashi abinci mai kyau a bashi tarbiya, ya kuma kamata a ce akwai likita idan akwai wata matsala domin kasashen Sahel matsalolinsu duk daya.”
Shi dai wannan tallafi zai zo ne daga Bankin Duniya.
Ga karin bayana a rahoton Souley Moumouni Barmah: