Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari a Yakin Diffa a Jamhuriyar Nijar


Mutanen da suka mutu sun wuce adadin da aka fadi

Wasu maharan sun kai hari garin na Ala dake kauyen Geskeru a yankin Diffa a jamhuriyyar Nijar.

Kimanin mutane goma sha uku ne maharan suka yiwa yankan Rago tare da kone kone a garin na Ala,dake yakin na Diffa, yayin da mutane uku suka tsira da raunuka.

Wani mazaunin garin Diffa, Malam, Isiya Ibrahim, ya shedawa muryar Amurka, cewa mutanen da suka mutu da wadanda suka samu raunuka sun wuce adadin da aka fadi.

Hukumomin garin Diffa, basu yi kasa a gwiwa ba sun garzaya yankin a lokacin da suka samu labarin afkwuwar wannan tu’annati domin yin ta’aziya da ganewa idanu da tautaunawa da jama’ar garin domin sanin matakin daya kamata a dauka.

Shi kuwa Malam, Mairu Ligari, Shugaban majalisar mashawarta ta jahar Diffa, ya ce yakamata a sake daura damara wajen yaki da 'yan ta'adda, amma yana mai cewa abun da kamar wuya sanya jami'an tsaro a tsawon kilomita 300, nisan iyakar Najeriya, da jahar Diffa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG