Kasancewar Nijar cikin kasashen da suka yi fice a duniya ya kayyade irin cigaban da aka samu daga alif dari tara da sittin zuwa yau duk da matsalolin tabarbarewar tattalin arziki a baya bayan nan.
Shugaba Issoufou yace duk da matsalar tsaro da matasalar canjin yanayi da faduwar darajar ma'adanai a kasuwannin duniya, tattalin arzikin kasar ya samu cigaba da kashi shida cikin dari.
To sai dai masu sharhi irin su Sani Adamu nada ja akan furucin shugaban. Yace lokacin jamhuriya ta farko akwai masana'antu barkatai amma a kwana a tashi yau babu su, inji Adamu. Baicin hakar uranium da man fetur babu wasu abubuwa na sarafawa cikin shekaru 56 da kasar ta samu 'yanci daga Faransa.
Sani Adamu ya cigaba da cewa tattalin arzikin kasar ya ta'allaka ne akan kasashen waje. Kasar bata cika fitar da wasu albarkatu ba sosai, inji Adamu. A fannin cimaka yace har yanzu kasar bata samu yadda zata ciyar da duk 'yan kasar ba. Duk shekarar da zara damina bata yi kyau ba sai kasar da fita waje neman taimakon abinci
Kakakin jam'iyyar PNDS dake mulkin kasar Asumana Muhammadou na cewa talakawa su ne shaidu dangane da cigaban da aka samu a Nijar. Yace a je wurin jama'a da mazauna karkara a tabbatar da abun da aka fada.
To sai dai wani mazaunin Yamai, Imam Mato, na ganin akwai bukatar sake salon tafiya domin talakan Nijar ya mori arzikin kasarsa. Ya kira shugabannin su daina cin hakkin talaka.
Dangane da tsaro shugaba Issoufou ya jinjinawa mutanen yankin Diffa saboda irin halin da suka shiga sanadiyar hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram. Yace nan ba da dadewa ba sojojin kasar da kawayenta zasu murkushe 'yan kungiyar Boko Haram.
Daga karshe shugaban na Nijar ya yabawa Amurka bisa ga tallafin da take ba dakarun Nijar a yakin da suke yi da 'yan Boko Haram.
Ga karin bayani.