Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta soke tsarin karbar takardar visa tsakaninta da kasashen Afirka, domin ba wa ‘ya'yan nafiyar damar shiga kasar ba tare da wata matsala ba.
Har ya zuwa makon jiya shigowa Jamhuriyar Nijar daga wasu kasashen nahiyar Afirka wani abu ne da ba ya yiyuwa ga ‘ya'yan wadannan kasashe, sai da takardar visa.
Ganin yadda wannan tsari zai taimaka wajen karfafa cudanya a tsakanin ‘ya'yan nahiyar ta Afirka, ya sa shugaban kasar Nijar Issohou Mahamadou ya soke takardar Visa, don bai wa dukkan Afirkawa damar shigowa Nijar, kamar 'yan kasa, wato tamkar suna gida, kamar yadda Ministan harkokin waje Kalla Hankourao ya tabbatarwa Muryar Amurka.
Masu rajin kare hakkin dan adam sun yaba da wannan tsari, ko da yake, sun ce akwai bukatar a yi taka-tsantsan don gudun fadawa tarkon masu tayar da hankali.
Salissou Amadou na CCA, daya daga cikin masu rajin kare hakkin dan adam, ya yaba da wannan yunkuri da suka dauka, matsayin wata alamar mutunta ‘yanci ne.
Yanayin tabarbarewar tsaron da ake ciki a yau a kasashen Afirka sanadiyar ta’addancin da ya addabi duniya, wani abu ne da ya kamata a yi la’akkari da shi wajen tafiyar da wannan sabon tsari.
A saurari cikakken rahotun wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum