Shugabancin tafiyar da ragamar rundunar hadin gwiwa ta 5G Sahel, ya koma hannun Jamhuriyar Nijar.
An nada mataimakin shugaban rundunar sojin Gen. Oumarou Namata Gazama ne domin ya canji dan kasar Mauritania Gen. Hanena Ould sidi wanda wa’adin shugabancinsa na watanni 12 ke kammala.
Matakin da ya sa wasu ‘yan kasar Nijar ke ganin wannan canji, ya yi daidai, lura da cewa sabon kwamandan ya ba da gudunmowa sosai wajen karya karfin Boko Haram a yankin Diffa.
Tsarin shugabancin karba-karbar da kasashe 5 mambobin G5 Sahel suka shimfida ne, ya bai wa Jamhuriyar Nijar damar karbar madafin wannan runduna mai yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
Hukumomin tsaro sun bayyana wa wakilin Muryar Amurka cewa Namata ya cancanci wannan matsayi saboda kwarewa akan aiki, sannan mutun ne mai la'akari da hakkokin bil adama.
Yankin Sahel ya matukar dandana kuda a watannin da suka gabata sakamakon munanan hare-haren ta’addancin da ake fuskanta a kasashen Nijar, da Mali da kuma Burkina Faso, dalilin da ya sa wasu suka amince da canji kwamandan kasar Mauritania Janaral Hanane Ould Sidi.
Mai shari'a akan sha’anin tsaro malami a jami’ar Yamai, Farfesa Issouhou Yahaya ya gargadi sabon kwamandan rundunar ta G5 Sahel ya ce akwai babban kalubale a gabansa.
Janaral Oumarou ya yi karatun soja a kasashe irin su Faransa, China da kuma Najeriya, sannan a cikin gida ya rike manyan makaman soja a yankunan Yamai da Zinder, da Arewacin kasa, kafin a shekarar 2016 hukumomin Nijar suka dora masa nauyin jagorancin ayyukan tsaro a yankin Tafkin Chadi.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum