A karshen watan Fabrairun da ya gabata ne aka fitar da shi zuwa kasar Tunisia sakamakon fama da wata cutar da ta shafi zuciya kafin rai ya yi halinsa a wannan rana ta Talata 8 ga watan Maris na 2022.
Tsohon dan jarida a gidan rediyon gwamnatin Nijar, Alhaji Gremah Boukar ya yi aiki a hukumar USAID sannan ya taba zama wakilin Muryar Amurka haka ya kuma kafa kamfanin jaridar amfani mai zaman kanta kafin daga bisani ya bude gidajen Rediyo amfani a jihohin Yamai Damagaram Diffa, Maradi da Tahoua.
Dan jarida a gidan Rediyon Amfani Issouhou Maman ya yi jimamin rashin inda bayyana rasuwarsa a matsayin wani babban rashi mara misaltuwa.
Dan asalin gundumar Maine Soroa ta jihar Diffa, Alhaji Gremah Boukar dan jarida ne da ya yi fafutukar kare dimokradiya, ya taka rawa a fagen siyasar Nijar inda a wani lokaci ya wakilici al’uma a majalisar dokokin kasa.
Ya kuma sha samun lambar yabo a kan aikin jarida cikin gida da waje haka kuma kafin ya rasu shi ne shugaban kungiyar RTIN ta mamallaka gidajen Rediyo da Television masu zaman kansu na kasa baki daya.
Dan shekaru 63 da haihuwa, Alhaji Grema Boukar Koura ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya'ya 6.
A ranar Asabar din dake tafe ne ake sa ran kawo gawarsa birnin Yamai kafin a yi jana’izarsa a washegari Lahadi.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: