Da yake gabatar wa Majalisar tsarin kasafin kudaden shekarar ta 2020, Ministan kudin jamhuriyar Nijar Mamadou Diop, ya bayyana cewa biliyon 2,266 na kudaden cfa ne gwamnatin Nijar ke fatan kashewa a shekara mai zuwa domin bukatun jama’ar kasar, abin da ya nuna an samu karin kashi 5.05 cikin dari idan za a kwatanta da kasafin shekarar da muke ciki.
Miinistan ya ce gwamnati za ta sa ido sosai don magance dukkan wani al'amari da ya shafi sha’anin haraji da na sauran hanyoyin biyan diyyoyin kasa. 'Yar Majalisar Dokokin kasa Mariama Manzo, ta ce ta yaba da kudirorin da gwamnati ta sa a gaba a karkashin wannan kasafi.
Sai dai matsalar tsaron da ta addabi jamhuriyar Nijar da makwabtanta shine babban abin damuwa, sakamakon yadda wannan lamari ke kara lakume makuddan kudade.
A watan gobe ne Majalisar za tayi mahawara akan wannan kasafi kuma a cewar ‘yan adawa zasu yi tsayin daka don ganin talakawa sun mori abubuwan da ake cewa an yi tanadi domin su.
Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum