A jamhuriyar Nijar jam’iyar PNDS Tarayya mai mulki ta kaddamar da wani shirin tayar da matasan jam’iyar daga barci, don ganin sun yi rajistar da za ta basu damar mallakar katin zabe, da kuma gudanar da wani taron kwanaki 2 da za'a zanta akan batutuwa da dama masu nasaba da aiyukan bunkasa tattalin arziki.
Sanin mahimancin kuri’un matasa a kowane irin zabe ya sa jam’iyar PNDS Tarayya shirya taron fadakarwa ga matasan ta da nufin ganar da su mahimmancin yin rajistar zabe.
Taron wanda aka shafe kwanaki biyu ana gudanarwa ya tattara daruruwan matasa daga jihohin Nijar, wadanda a karshe ke da alhakin isar da irin wannan sako ga takwarorinsu na yankunan karkara.
A bangaren kungiyar matasa na OJT, ta gayyato masana a fannin makamashi da kimiyya, aka tattauna akan mahimancin ilimi da batun samar da wadatar makamashi a matsayin wata hanyar ciyar da kasa.
Wannan shine karo na biyu da uwar jam’iyar PNDS ke shirya irin wannan taro domin wayar da kan matasa a game da nauyin da ya rataya a wuyansu a matsayinsu na manyan gobe.
Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
.
Facebook Forum