Kawo yanzu dai 'yan siyasa goma sha shida ne suka fito daga jam'iyyu daban daban suna neman dare kujerar shugaban kasa.
To saidai kafin su zama tabatattun 'yan takara sai kotun tsarin mulki ta tattancesu. Amma mai magana da yawun PNDS Tarayya yace su kam a shirye suke su tsaya takara. Ko 'yan takara nawa ne suka fito su zasu ci nasara domin talakawa sun ga aikin da jam'iyyarsu ta yi .
A jam'iyyar Model Lumana Alhaji Lawali yace su ma dan takararsu Hamma Ahmadu ya cika ka'idojin tsayawa takara. Yace duk takardun da suka cancanta sun saya sun cike kuma sun ajiyesu kamar yadda doka ta tanada.
A bangaren farar hula Iliya Dan Malam cewa ya yi a dai yi zabe ingantace mai adalci saboda a ganinsu dimokradiya bata da wata matsala a kasar.
Ga karin bayani.