Matsalar ruwan anfani yau da kullum ta addabi jama'a akudancin jamhuriyar Kamaru.
Karancin ruwa bai cika faruwa ba a kudancin kasar musamman a babban birnin kasar Yaounde da babban birnin cinikayya Douala.
Kimanin wata guda ke nan da jama'ar wannan bangaren Kamaru ke fama da karancin ruwa lamarin da ya jefasu cikin halin ni'yasu.
Yawancin iyaye da 'ya'yansu suna tashi ne cikin dare su shiga neman ruwan da zasu yi anfani dashi.
Saboda tsananin neman ruwa da iyaye ke sa 'ya'yansu yi wasu cikinsu basa samun zuwa makaranta domin suna can wurin neman ruwa suna tangareriya da bokatai..
Duk inda aka juya a birann Yaounde da Douala sai mutane ake gani suna yawo da jarkokin neman ruwa.
Wasu da aka zanta dasu sun ce ko gwamnati ta yi fushi da wanda yake kula da ma'aikatar ruwa saboda bai yi abubuwan da ya kamata ya yi ba. Gwamnati ta cireshi. Duk da haka wasu na ganin tuni yakamata gwamnati ta yi aikinta ba sai lokacin zabe ba.
Yara ma da basu samu ruwan wanka ba sun ce ba zasu iya zuwa makaranta ba. Haka ma wata mata wadda ko ruwan da zata ba yaranta su sha bata dashi tace sun rasa yadda zasu yi kasancewa babu ruwa ko na abinci ko na sha ko na yin sana'ar abinci.
Ga karin bayani.