A jamhuriyar Nijar kungiyar Alternative ta fitar da rahoto a game da halin da jama’a ke ciki a yankin Diffa, sanadiyar rikicin Boko Haram, inda rayukan mutane ke salwanta yayinda satar mutane ke karuwa, duk da irin matakan da hukumomi ke cewa suna dauka.
Makwanni sama da 3 kungiyar AEC ta shafe, tana gudanar da bincike domin tantance zahirin halin da al’umma ke ciki a jihar Diffa, yankin dake fama da rikicin Boko Haram.
Karancin tallafi daga kungiyoyin agaji ya sa jama’ar da Boko Haram ta tilastawa tserewa daga matsugunansu, suka soma rungumar wasu ayyukan dake barazana ga mahalli.
Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum