Sau biyu jere ambaliyar ruwa ke ruguza gidajen al’umar kauyen Borgo ta gundumar Balleyara lamarin da ake alakantawa da rashin dacewar filin da aka tsara garin tun farko. Daliki i ke nan da kungiyar Quatar Charity ta yanke shawarar gina wani gari sabo ful mai gidaje 100 da nufin kawo karshen wannan matsala.
Ministan cikin gida Bazoum Mohamed wanda ya jagoranci bukin damka wadanan gidaje a hannun wadanda aka yi domin su, ya jinjinawa wannan kungiya saboda a cewarsa ta yi abinda ya kamata takwarorinta su yi koyi da shi.
Wadanda Sashen Hausa ya yi hira da su, a wajen kaddamar da gidajensu sun bayyana frin cikinsu, da cewa suna daukar bukin damka wadanan gidaje tamkar wata ranar salla.
Seini Issoufou daya daga cikin wadanda suka ci moriyar wannan tallafi, yace “Ina godiya da muka samu wannan alheri a cikin garinmu. Ina yiwa Allah godiya kuma ina godewa wadanda suka yi dalilin samun wannan taimako. Mun yi murna sosai.”
A watan mayun 2017 ne kungiyar Quatar Charity ta kaddamar da wannan aiki dake matsayin na gwaji wanda kuma aka bayyana cewa ya lakume miliyan 1200 na cfa.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumoni Barma
Facebook Forum