Shugaban cibiyar Dr Mustapha Musa ne ya bayyana a wata hira da manema labarai a garin Gombe inda ya bayyana cewa cutar ta sake bulla a jihar.
An gano kananan yaran dake dauke da cutar ne tsakanin watan Janairu da Afrilu na wannan shekarar ta 2013, a kananan hukumomin Dukku, Yamaltu-Deba da Shongom.
Bisa ga cewarshi, cutar kuturta a jihar ta ragu sosai. Yace a sami mutane kusan 100 dauke da cutar a shekara ta 2012 daga 120 da aka samu dauke da cutar a shekara ta 2011, sai dai a wannan lokacin an sami kananan yara dauke da cutar.
Dr Musa ya bayyana takaicin ganin yadda ba a maida hankali wajen shawo kan cutar ba duk da yawan barnar da take yi har ta kai ga kama kanannan yara. Yace, an dauki matakai domin rage hanyar yaduwar cutar.
Yayi bayani cewa cutar na yaduwa ta hanyar atishawa da tari, kuma tana daukar kimanin shekaru uku zuwa goma kamin ta bulla a jikin mutum.
Shugaban cibiyar yaki da cututukan yace, an kafa wuraren bincike a kananan hukumomi 11 na jihar yayinda kuma ake yiwa masu fama da cutar jinya kyauta.