Malam Ibrahim Sani Albani babban sakatare na ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar Niger ya ce a cikin irin rikicin dake faruwa a Afirka Ta Tsakiya sai kura ta lafa za'a san yawan mutanen da rikicin ya rutsa dasu amma a nasu sanin kawo yanzu dan Niger daya ne suka tabbatar ya rasa ransa. Kodayake ba'a san adadin 'yan Niger dake kasar ba amma shaidu sun ce akwai daruruwan 'yan kasar a makale a wasu garuruwa da dama. Ita kasar Afirka Ta Tsakiya ta fada cikin rikicin kabilanci da na addini ne. Sakataren ya sake tabbatar da kariyar da 'yan kasar Niger ke samu daga sojojin Faransa da na kasar Chadi masu aikin kwantar da tarzoma.
Rikicin ya fi tsamari a Bangui babban birnin kasar. Wani Abdullahi daga jihar Tawa dan Niger mazauni garin ya ce lamarin ya baci kuma ba da dadewa ba aka kai masu hari a unguwar da suke. Ya ce an kone gidajen Musulmai an kuma kashe wasu cikinsu. Akwai kuma wadanda suka samu rauni. Mutumin ya ce sojojin Chadi suna karesu amma na Faransa babu ruwansu da kowa. Duk Musulmin dake cikin birnin Bangui suna gudu. Ya ce suna bukatar taimakon jirgin da zai zo ya kwashesu komawa Niger.
To sai dai sakataren maa'ikatar harkokin wajen Niger ya ce kwashe 'yan Niger daga Afirka Ta Tsakiya zai yi wuya domin basu iya tantance ko su nawa ne ke kasar ba. Ya ce ba abu ba ne da ba za'a iya yi ba sai dai matsalar ita ce kasar Niger bata da jakada a kasar.Kan adadadin 'yan Niger din sakataren ya ce wasu sun ce sun kai 1000 wasu kuma sun ce 700. Ya ce idan sun samu ma sun je wanene suka sani dan Niger ne ko ba dan Niger ba.
Abdullahi Mamman Ahmadu nada karin bayani.