Kawo yanzu alhazai dari biyar ne daga cikin kimanin maniyatta dubu uku daga jihar aka samu kaiwa kasar Saudiya a cikin kasa da mako guda da fara aikin jijgilarsu.
Wasu daga cikin alhazan sun ce suna neman mafita a wurin Allah duk da an gaya masau suna cikin jirgi na uku wanda har lokacin da suke magana basu ganshi ba. Wani an kirashi cewa zasu tashi ranar Asabar sai kuma tashin bai yiwu ba. Har yanzu suna sauraren ranar da zasu tashi.
Sun yi korafin cewa tsarin da aka fito dashi bai cancanta ba domin alhazan sun yi fiye da kwana hudu babu labarin tafiya. Kamata yayi su iso sansanin da ake ajiye alhazan ranar da zasu tashi.
Hukumar jin dadin alhazan ta jihar Nejan tace tana iya kokarinta domin tabbatar da an kwashe alhazan kafin kurewar lokaci.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Sani Awal ya mayarda martani kan korafin alhazan yace tun farko sun bada umurni kada wani alhaji ya shigo sansanin sai an kirashi. Wadanda suka fito daga wasu kananan hukumomi ba'a kirasu ba. Duk wadanda lokacin tashinsu yayi ana kiransu. Yace akwai alhazai fiye da dubu daya da basu kira ba.
A makon jiya ne gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya cire mataimakinsa daga matsayin amirul hajin jihar a daidai lokacin da ake jigilar maniyattan.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.