Cruz wanda Sanata ne mai raayin ‘yan Mazan jiya mai kuma wakiltan jihar Texas, yayi nasara da samun kashi 28 inda ya buge attajirin nan Donald Trump wanda ya samu kashi 24.
Shiko Sanata Marco Rubio na jihar Florida ya samu kashi 23, sai dai wannan kuri'ar da sanata Rubio ya samu ya baiwa mutane mamaki, domin ba wanda ya zaci zaibi Donald Trump kusa da kusa haka.
Sauran yan takaran dai ba wanda ya samu maki mai lamba biyu.
A can cikin jamiyyar Democrat ko tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka ce Hilary Clinton ta lashe zaben da yar tazara kadan inda ta buge abokin karawar ta dake binta kud da kud, wato Banie Sanders.
A kalla a ciikin kashi 80 na masu jefa kuri'ar, Hillary ta samu kashi 50 yayin da Vermont Banie Sanders ya samu kashi 49, shiko tsohon gwamnan jihar Maryland Martin O’Malley ya samu kasa da kashi daya, abinda yasa yace yau din nan zai bayyana saukar daga wannan takarar.
Haka shima tsohon gwamnan jihar jihar Arkasas Mike Hukabee yace zai bayyana saukar sa daga takara, wanda ko a shekarar 2008 shine ya lashe zaben fidda gwani a jihar ta Iowa
Wannan sakamakon dai ya fara nuna inda hankalin masu jefa kuria ka iya karkata, kuma ya fara nuna cewa zai fara dakile yawan hasashe da Shashi fadin da ake tayi game da zaben gaba dayan sa.
Rahotanni sun bayyana cewa masu jefa kuria sun fito sosai, kuma ‘yan takara sunyi wa masu jefa kuria da sauran jama'a bayanin su na karshe kafin a fara jefa kuri'a.