Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firai Minista Benjamin Netanyahu na Ziyarar Aiki a Kasashen Turai


Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu wanda ke ziyarar aiki a kasashen turai yace kasar Iran na iya haddasa kara kwararar 'yan gudun hijira a kasashen Turai idan ba a dauki mataki ba

Firai Ministan Isra’ila Benjamain Netanyahu zai gana da shugaban kasar Faransa yau Talata a birnin Paris a cigaba da yunkurin neman goyon bayan shugabannin kasashen Turai na yin gyara a yarjejeniyar kasa da kasa da aka cimma akan ayyukan nukiliyar Iran.

Netanyahu ya fara yada zango a kasar Jamus jiya Litinin, a ziyarar kwanaki uku da yake yi a kasashen Turai, inda ya gargadi shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel cewa, shish-shigin da Iran ke yi a Gabas ta Tsakiya zai iya haifar da kwararar ‘yan gudun hijira.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai na hadin guiwa da Merkel shugaban kasar Isra’ilan ya ce Tehran tana neman gudanar da gangamin addini a kasar Syria da galibi ‘yan Shi’a ne, ta wajen amfani da mayaka ‘yan shi’a dake karkashin ikonta, wajen sauya ra’ayin Musulmi ‘yan Sunni.

Markel ta amince da cewa ayyukan Iran a Gabas Ta Tsakiya abin damuwa ne, sai dai ta kare yarjejeniyar ayyukan nukiliyar da tace hanya ce ta toshe kafar cimma burin Iran na mallakar makaman nukiliya, da kuma wadansu kudurorin da take neman cimmawa a yankin.

Netanyahu zai kuma gana da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yau Talata da kuma Firai minister kasar Burtaniyya Theresa May gobe Laraba idan Allah Ya kaimu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG