Rundunar ta samu cafke wasu mutane guda biyu da suka shahara wajen sace mutane su yi garkuwa dasu domin neman kudin fansa.
Sakamakon sace mutane ke kara ta'azara a jihar ya sa kwamishanan 'yansandan jihar ya kaddamar da wani sintiri na musamman. Kakakin rundunar ASP Elkana yace dalilin sabon tsarin nasu jami'ansu sun shiga wani kauye da ake kira Masallacin Zaki a karamar hukumar Mashegu inda masu sace mutane suke boyewa. A can ne suka samu kama mutane biyu tare da samun miyagun makamai.
'Yansandan na kan bincike kuma da zara sun kammala zasu gurfanar dasu gaban shari'a.
Bayan yin sintiri rundunar tana gudanar da tarurruka da kungiyoyin jama'a a yankunan karkara domin tabbatar da an samu biyan bukata a yaki da sace mutane.
Wani jami'in 'yansanda dake kula da garin Kontagora Sagir Yusuf Garba yayinda yake gudanar da taron fadakar da jama'a ya shaidawa Muryar Amurka cewa idan ana son cimma ingantacen tsaron kasa dole ne a sa al'umma ciki. Yace dole ne kowa ya bada gudummawarsa domin a shawo kan matsalar.
Yanzu dai kwamitin 'yansanda da na kungiyoyin fararen hula suna sa ido sosai domin yakar matsalar sace mutane a jihar musamman akan shiga da ficen baki a yankunan karkara har ma da lura da dalibai 'yan makaranta dake gararamba akan titi a lokacin da ya kamata suna makaranta suna karatu.
Yanzu dai duk dan makarantan da suka ga yana gararamba lokacin da yakama a ce yana makaranta zasu kama shi.
Ga karin bayani.