An bayyana cewa ganin yawan cututtukan da ke addabar mutane a Lagos, ya sa aka kafa hukumar saka ido kan ingancin irin ruwan da aka samar wa jama’a. Shugaban Hukumar Kula Da Ingancin Ruwa ta jahar Lagos Arc. Ahmed Kabi Abdullahi ne ya bayyana hakan ma abokin aikinmu Ladan Ibrahim Ayawa lokacin da ya kawo ziyara Muryar Amurka.
Arc. Abdullahi y ace kula da tsafta da kuma lafiyar ruwa na da matukar muhimmanci wajen kare lafiyar mutane ganin yadda cututtuka iri-iri kan rabe da ruwa su yi ma mutane illa. Hakan ya sa, in ji shi, gwamnatin Lagos ta yanke shawarar kafa hukumar ta kula da ingancin irin ruwan da kamfanoni masu zaman kansu ke sayar ma jama’a.
Ga cikakkiyar hirar: