Shugabar Majalisar Wakilan Amurka, ‘yar jam’iyyar Demokarat, Nancy Pelosi, ta sanar, a hukumance, da shirin fara binciken tsige Shugaba Donald Trump, da zargin cewa ya nemi taimakon gwamnatin wata kasa a kokarin da yake yi na ganin an sake zaben shi a badi.
A cewar Pelosi, wannan mataki da shugaban ya dauka, ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, saboda haka ya zama dole a bincike shi, domin babu wanda ya fi karfin doka.
Shugabar Majalisar ta bayyana wannan matsaya ne, bayan da suka gudanar da wata tattaunawa ta sirri da shugabannin majalisar wakilai na bangaren ‘yan Demokarat, yayin da adadin wadanda ke kiran a kaddamar da binciken tsige Trump ya karu a yau Talata.
Sai dai Shugaban na Amurka ya kwatanta wannan mataki na ‘yan Demokarat da bita-da–kullin siyasa.
A gobe Laraba, Shugaba Trump ya ce zai saki takardar bayanan da suka tattauna da shugaba Zelenskiy na kasar Ukraine, ba tare da an tace ba.
Ana zargin Shugaba Trump da yin kira ga takwaran aikinsa na Ukraine da ya kaddamar da bincike kan dan tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden – da zimmar ganin an tono wata badakala da za ta bata wa Biden suna a matsayinsa na wanda ake ganin da shi Trump zai yi takara a badi.
To a halin da ake ciki, mambobin majalisar wakilai da ta Dattawa na bin sahun jam’iyyunsu wajen mayar da martani kan wannan sanarwa ta Pelosi.
Dan Republican kuma shugaban masu rinjaye a majalisar ta Dattawa, Mitch McConnel, na zargin ‘yan Demokarat da yin riga-malam-masallaci wajen bayyana Shugaba Trump a matsayin mai laifi, yana mai cewa abin da ya faru a jiya, wani shiri ne na neman dalilin tsige Trump.
Sai dai shugaban kwamitin da ke sa ido kan kwamitocin majalisar wakilai, Elijah Cummings, wanda dan jam’iyyar Demokarat ne, ya fada wa ‘yan Republican cewa su tuna cewa “tarihi zai nuna cewa sun yi watsi da aikinsu na kare kundin tsarin mulkin kasar, idan suka kau da idonsu suka fifita jam’iyya akan kasarsu.”
Facebook Forum