Matashiyar nan mai fafutuka ‘yar kasar Sweden, Greta Thunberg, ta caccaki shugabannin duniya a jiya Litinin a babban taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ta yi kira da a dauki matakan magance sauyin yanayi, saboda matsalolin da hakan ke haifarwa.
“Mutane na wahala, mutane suna mutuwa, halittun duniya na ta gushewa, mun shiga wani kangi na gushewa daga doron kasa, amma abin da za ku zauna kuna magana akai shi ne batun kudi da bunkasar tattalin arziki? Inji Thunberg.
Ta kara da cewa, ilimin kimiyya ya bayyana wannan matsala karara tun shekaru 30 da suka gabata , amma har yanzu ba sa yin komai akai.
Thunberg cikin murya mai cike da tausayawa, ta ce" kun gaza a idonmu! Amma matasa sun fara fahimtar cin amanarku. "Idanun manyan gobe na kanku. Kuma idan kuka zabi ku ci gaba da gazawa a idonmu, ba za mu taba yafe maku ba."
‘Yar shekaru 16, Thunberg ta gargadi shugabanni da firayim ministoci sama da 60 da suka hallara a zauren Majalisar don taron kolin, inda ta ce matasa ba za su bar ku ba "ku tserewa wannan batun."
Facebook Forum