Daga cikin abubuwan da wadannan kwararru na kasar China zasu taimaka wajen kakkafawa, har da masana'antun sarrafa tumatur, da barkono da wasu kayan danye, maimakon a rika fita kasashen waje da wadannan kayayyaki ana sarrafa musu, sannan a komo da shi ana sayarwa da tsada.
A bayan kuma da aka kashe wani dan kasar China mai aikin kwangila kwanakin baya a jihar ta Borno, 'yan kasar duk sun wkashe kayayyakinsu sun gudu. Yanzu kamfanin dake wannan aikin, ya yarda cewa za a tura matasa 'yan jihar Borno wadanda suke da takardun kammala karatunsu a aikin injiniya ko gini ko makamancin hakan, zuwa kasar China domin kamfanin ya koya musu dukkan matakan irin wannan aiki, su komo su na gudanarwa da kansu a jihar.
Makasudin wadannan ayyuka dai shi ne rage yawan matasan dake zaune babu aikin yi, domin hana su shiga ko fadawa cikin tarkon tsagera da zasu nemi yin amfani da su domin kawo tashin hankali.
Haruna Dauda ya aiko da karin bayani kan wannan.