Mutane da dama sun goyi bayan matakin da majalisar wakilan Najeriya ta dauka game da hukumomin zaben jahohi
WASHINGTON, DC —
Wakilin Sashen Hausa a Sokoto Murtala Faruk Sanyinna ya jiwo ta bakin jama’a game da matakin da Majalisar Wakilan Najeriya ta dauka na soke hukumomin zaben jahohi da mayar da su karkashin hukumar zabe ta kasa INEC. Amma Murtala ya fara ne da tuntubar shugaban sashen nazarin kimiyar siyasa na jami’ar Usmanu Dan Fodio dakta Yahaya Tukur Baba domin yayi bayani game da tasiri da kuma alfanun kafa hukumomin zaben jahohin a can baya da kuma rusa su a yanzu: