Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nan Ba Da Jimawa Ba Tinubu Zai Daure Duk Wanda Ya Bayyana Masa Adawa - Atiku


Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/Atiku Abubakar)
Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/Atiku Abubakar)

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, dan takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP a zaben 2023, yace kame da gurfanarwa maras tushe ta baya-bayan nan da aka yiwa Omoyele Sowore da Usman Yusuf su ne sabbin nau’ukan cin zarafin da ake yi wa jagororin adawa.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya koka da abin da ya bayyana da tsarin rushe bangaren hamayya da gwamnatin Tinubu ke amfani da shi.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, dan takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP a zaben 2023, yace kame da gurfanarwa maras tushe ta baya-bayan nan da aka yiwa Omoyele Sowore da Usman Yusuf su ne sabbin nau’ukan cin zarafin da ake yi wa jagororin adawa.

“Kame da gurfanarwa maras tushe da aka yiwa Omoleye Sowore ne sabon shafin da aka bude na yakin da ake yi babu kakkautawa. Yanzu sun ga ya dace su kara Farfesa Usman Yusuf - fitacce wajen sukar gwamnatin nan - a cikin wannan mummunar aniyar ta su.”

Sowore, wanda ya kasance shugaban gangamin juyin juya hali mai taken #revolutionnow, ya mutunta gayyatar ‘yan sanda a ranar Litinin 27 ga watan Janairun da muke ciki, inda ya amsa tambayoyi a sashen binciken manyan laifuffuka na rundunarsu. A jiya Alhamis, kotu ta bada belin Sowore a kan kudi Naira miliyan 10 da mai tsaya masa mutum daya wanda shima zai biya makamancin adadin.

Haka kuma a ranar Larabar da ta gabata, hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, ta kama tsohon babban sakatare a hukumar inshorar lafiya ta kasar, Farfesa Usman Yusuf wanda ya yi fice wajen sukar gwamnatin Tinubu, a kan zargin aikata zamba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG