Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangaren Shari’a Ne Babbar Barazana Ga Dimokiradiyar Najeriya - Atiku


Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/Atiku Abubakar)
Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/Atiku Abubakar)

Atiku ya kuma yi zargin cewa babu wanda zai takawa sauran rassan gwamnati burke a kan wuce gona da irin da suke yi.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa bangaren shari’a ne babbar barazana ga tsarin dimokiradiyyar kasar.

Ya bayyana hakan ne jiya Litinin a Abuja, a matsayinsa na alkalin muhawara a wani taron kasa a kan karfafa tsarin dimokradiyya a Najeriya.

A cewarsa, sauye-sauye da aka gudanar da nufin magance gangancin bangaren shari’a bai haifar da wani sakamako ba.

“Alamu na nuna cewa bangaren shari’ar ya maye gurbin masu kada kuri’a wajen zaben shugabanninmu. An shigo da bangaren shari’a wajen sasanta rikicin zabe ne da nufin tabbatar da zabin masu kada kuri’a.

“Sai dai bangaren shari’armu, harma a can koli, kan murda al’amura domin gano dabarun da zai yi amfani dasu wajen tauye zabin masu kada kuri’a a maimakon tabbatar musu da shi.

Atiku ya kuma yi zargin cewa babu wanda zai takawa sauran rassan gwamnati burke a kan wuce gona da irin da suke yi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG