Baicin dalilin habaka shuka shinkafa a cikin gida akwai kuma dalilin hana shigowa da gurbatacciyar shinkafa wanda ya saba faruwa can baya.
Babban kwantrolan hukumar hana fasakwauri Kanar Hamid Ali yace gwamnati na barin a shigo da shinkafar ta teku inda hukumar kula da lafiyar abinci da magunguna NAFDAC take da kayan gwajin shinkafar da ta shigo ta teku.
Yace batun shinkafa an dade ana kai da kawowa.Wadanda yakamata su sani sun sani wadanda kuma saboda rashin sani suna ta yin korafe korafen da basu kamata ba. Yace ainihin gaskiyar ita ce gwamnati bata hana shigowa da shinkafa ba. Sai dai ta hana shigowa da shinkafa ne ta iyakokin kasa.
Kanar Hamid Ali yace akwai gurbatacciyar shinkafa dake shigowa ta iyakokin kasar saboda NAFDAC bata da naurorin gwaji akan iyakoki. Naurorin gwajinta suna tashoshin teku ne. Dalili ke nan da gwamnati ta ce duk wanda zai shigo da shinkafa sai dai yayi anfani da hanyar teku inda NAFDAC zata iya yin gwajin da ya dace su tabbatar shinkafar lafiyayyiya ce kuma ana iya cinta..
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.