Shirye shiryen sun hada da amfani da jiragen kasa wajen daukan kaya daga tashohin doron kasa don kaisu bakin teku, inda za’a kai ketare don sayarwa. Ko kuma kayan da ‘yan kasuwa suka sayo daga kasashen waje a sauke musu a tashoshin dake sassa daban daban ciki kuwa harda Jos da Funtua da Kano da Maiguri.
Bangaren jiragen sama kuwa gwamnati zata kammala gyaran jiragen sama musammamma na Abuja, inda za a bada jinginarsu ga ‘yan kasuwa. Ministan zirga-zirgan jiragen Hadi Sirika ya nuna damuwa cewa tsohon gwamnatin Jonathan ta ciwo bashin gina sabbin gine gine a filayen jiragen sama hudu, inda ginin da tayi a Abuja ya zama aikin baban giwa.
Domin daga cikin matsalolin da kamfanin jiragen sama na Emirate suka bayar shine babu isasshen gurin da zasu saukar da babban jirgin sama, dole sai dai su rinka zuwa da karamin jirgi wanda kuma babu riba a garesu. A cewar Hadi Sirika, fadada gurin zai taimaka wajen samun manyan kamfanonin su rika zuwa da jiragensu.
Shugaban hukumar kasuwanci ta teku hada hadar teku Dakta Hassan Bello, ya nanata muhimmancin ‘yan kasuwar Najeriya da su mayar da hankali wajen fitar da haja waje don samarwa kasar kudin musaya.
Domin karin bayani.