Wannan mataki ya sanya jihar cikin jerin jahohin Najeriya da suka amince da wannan doka da zarar gwamnan jahar Akinwumi Anbode ya sanya hannu akan ta. Tuni dai jama’a suka fara yin maraba da wannan doka.
‘yan Majalisar jahar Lagos sun amince da dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da yin garkuwa da wani ko wata tare kuma da sanadiyyar mutuwar wanda aka kama. Duk da yake za a jira sa hannun gwamnan jahar kafin a tabbatar da wannan doka.
Hukumomin Najeriya wanda suka hada da gwamnatin tarayya zuwa jahohi a kokarinsu na ganin an kawo karshen sace mutane a yi garkuwa da su wanda yanzu haka ya zama ruwan dare a Najeriya, ‘yan Majalisun jahar Lagos sukayi wannan yunkuri domin shiga jerin takwarorinsu da suka riga suka kafa dokar.
Kakakin Majalisar Dokokin Jahar Lagos Hon. Mudashiru Obasa, shine ya gabatar da wannan kuduri sakamakon yawaitar sace-sacen jama’a da ake yi a birnin Lagos.
Ko a kwanannan sai da aka sace wani basarake a yankin Ikorodu na birnin Lagos, wanda daga bisani aka gano shi bayan da iyalinsa suka biya makurdan Miliyoyin Naira domin a sako shi, daga bisani dai jami’an ‘yan sanda sun kamo wadanda suka sace basaraken. Bayan wannan kuma sau biyu ana kai hari wasu makarantun kwana inda nan ma ake garkuwa da dalibai lamarin da kan haifar da tashin hankali tsakanin malamai da dalibai da iyaye.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin daga Lagos.