Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Fara Karawa A Wasan Tseren Dusar Kankara A Beijing


Wasan tseren dusar kankara
Wasan tseren dusar kankara

Samuel Ikepfan ne yake wakiltar kasa mafi yawan al’umma a Afrika, duk da cewa yana kuma da katin shaidar zama dan kasa a Faransa.

A karon farko, Najeriya ta shiga wasan gudu mai dogon-zango na tsere a dusar kankara, a gasar wasannin Olympic ta shekarar 2022 da ake gudanarwa a Beijing.

Samuel Ikepfan ne yake wakiltar kasa mafi yawan al’umma a Afrika, duk da cewa yana kuma da katin shaidar zama dan kasa a Faransa.

A ranar Litinin, Ikpefan ya bayyana a shafinsa na Instagram dauke da koren mayafi da kuma tutar Najeriya mai kalar kore da fari a gabansa, yana cewa ina fatar zan yi iya bakin kokarina”.

Dan shekara 29 da haihuwa, ya ce “da abinci ko kuma waka, na kasance cikin al’adun Najeriya a ko da yaushe.”

Tsohon zakaran gudun gajeren zango rukunin matasa a Faransa, wanda ya girma a yanki mai duwatsu na Annamasse, ya ce yin wasan tseren dusar kankara wa Najeriya, zai taimaka masa wajen samun alaka mai karfi da kasar mahaifinsa.

Ya ce yana fatar ya zama abun koyi a samu sabbin masu yin wasan deben kankara ‘yan Najeriya. Ya kara da cewa burinsa na Olympic, zai kai kololuwa a gasar Milano Cortin da za a yi cikin shekarar 2026.

A gasar Milano Cortina ta shekarar ta 2026, an nada ni kyaftin na wata kungiya da ta kunshi ‘yan wasa matasa uku daga Najeriya, amma suke zama a wasu kasashen. Aiki na shi ne in yi musu bayanin yadda abubuwan suke, sannan in taimaka musu a atafiyarsu ta zuwa Olympic”, a cewarsa.

A cikin watan Janairun 2021 ne, a karon farko, Ikpefan ya shiga gasarsa ta farko ta kofin duniya, a garin Falun, na kasar Sweden.

Najeriya ta yi suna a wasan Pyeonchang a shekarar 2018, lokacin da ‘Yan wasanta suka cancanci fafata gasar ninkayar kankara akan falanke da daga karfe mai nauyi.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG