Hakan ya fito ne a wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gwamnatin kasar, kuma shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus da shugaba Buhari ya kafa, Boss Mustapha.
Manajan kota kwana na kwamitin yaki da cutar coronavirus Dr. Mukhtar Muhammad, ya ce an sa dokar hana shigowa da kuma killacewa bayan shigowa Najeriya ne domin kare lafiyar 'yan kasar da kuma tabbatar da lafiyar masu shigowa kasar.
Dr. Mukhtar ya kara da cewa gwamnati ta tanadi hukunci da za a yi wa duk wadanda suka karya dokar da ya hada da kwace passport na tafiye-tafiye ga 'yan Najeriya da kuma kwace visa ko takardar shaidar zama a kasar ga wadanda ba yan Najeriya ba.
A nashi bangaren, kakakin hukumar shige da fice ta Najeriya James Sunday, ya ce hukumarsu na taka rawar gani wajen amfani da na'urorin dake tantancewa da kuma zakulo duk wadanda suka shigo kasar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Domin karin bayani saurari rahotan Hauwa Umar.