An samu wasu ‘yan takara ‘yan kalilan na shiyya da su ka ce su na bukatar a gudanar da zaben, amma su din ma yawanci gwamnoni sun rarrashe su su ka janye.
Daya bayan daya masu takara su ka rika janyewa don mara baya ga jerin sunayen da gwamnoni su ka amince da su da a ciki akwai wanda a ka yi amanna dan takarar shugaba Buhari ne, wato sabon shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.
Gabanin tabbatar ma sa nasarar, Sanata Adamu ya ce ai ba ya shakkar a shata dagar zabe.
Na ji a na ta sharhi a taron cewa in ka debe Abdullahi Adamu sauran shugabannin gwamnoni su ka ba da sunayensu da kauce wa jerin sunayen da shugaba Buhari ya amince da su.
Hakan bijire wa shugaba Buhari ne ko kuwa a’a, shugaban ya fice daga dandalin taron ba tare da shaida yanda a ka yi ta janyewa ba da nuna don mutunta shugaban ne.
Gwamnoni ne su ka dora jama’arsu a karagar jam’iyya da ke nuna alamar haka za su sake yi a tsaida dan takarar shugaba da ba lallai sai wanda shugaba Buhari ke kauna ba.
Shin APC ta bar baya da kura ko an yayyafa wa kurar ruwa?
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: