Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Na Zawarcin Masu Zuba Jari


Buhari yayin gabatar da jawabinsa a Paris (Facebook/Fadar gwamnatin Najeriya)
Buhari yayin gabatar da jawabinsa a Paris (Facebook/Fadar gwamnatin Najeriya)

“Darasin da muka koya daga annobar nan, ya sa mun kara kaimi wajen magance illolin da annobar ta haifar.” In ji Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga masu zuba hannun jari na kasa da kasa da su karkato da hankulansu kan kasar duba da yadda tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da bunkasa.

Buhari ya yi wannan kiran ne yayin gabatar da jawabinsa a wajen taron kasa da kasa a birnin Paris wanda ya mayar da hankali kan kulla alakar kasuwanci da janyo hankalin masu zuba hannun jari.

Taken taron shi ne, “Yin hange bayan annoba,” wato COVID-19.

A cewar Buhari, Najeriya na da kayayyakin more rayuwa da za su tallafawa masu zuba hannun jari, da ilimin fasahar sadarwa da ke tafiya da zamani da kuma samar da damar zuba hannun jari kai-tsaye karkashin shirin nan da ake kira FDI.

Shugaba Buhari ya kara da cewa tattalin arzikin Najeriya na samun tagomashi da daidaito, a wani mataki na ganin ya samu damar yin gogayya da sauran kasashe, ta yadda ‘yan kasuwa da abokanan huldar kasuwanci za su iya cin moriyarsa.

“Darasin da muka koya daga annobar nan, ya sa mun kara kaimi wajen magance illolin da annobar ta haifar.” Wata sanarwa da Kakakin Buhari Femi Adesina ya fitar ta ce.

“Ina mai ba ku tabbacin cewa, gwamnatinmu na kan hanya madaidaiciya wajen bunkasa fannoninta.” Buhari ya kara da cewa.

Daga cikin manyan ‘yan kasuwan Najeriya da suka halarci taron akwai shugaban kamfanin Oriental Energy Resources Mohammed Indimi, shugaban kamfanin BUA Group, Abdul Samad Rabiu, shugaban bankin Zenith Bank Jim Ovia da dai sauransu.

XS
SM
MD
LG