Ministan cikin gidan Najeriya Janar Abdulrahaman Dambazzau ya amnice a kori Indiyawa 36 da suka shiga kasar da takardar biza ta jabu.
Baicin indiyawan akwai wasu 'yan Koriya biyu da su ma aka kora duk da cewa suna aiki da gwamnatin Zamfara ne bisa zargin cewa takardunsu na zama sun kare kuma ba su sabunta ba. Su 'yan Koriyan an gano cewa kwangilar su da gwamnatin Zamfara ya kare.
Gwamnatin Najeriya ta ce abun da Indiyawan da 'yan Koriya suka yi ya sabawa kundun tsarin mulkin kasar.
Dr Abubakar Kari, na jami’ar Abuja ya ce wannan abun an dade ana yi har ma, sauran kasashen duniya sun fara raina kasar saboda suna ganin komi kara zube ne, za su iya cin karensu ba babbaka.
Amma wasu 'yan Najeriya irinsu Sabo Gashua na kira a yi taka tsantsan musamman kan batun 'yan Koriya da aka ce takarsunsu sun kare ne kawai. Ya ce ya san wata da takardunta suka kare kuma yau shekara daya ke nan tana nema a sabunta mata amma shiru.
Kwararre kan harkokin diflomasiya Ambassador Suleiman Dahiru ya ce lamarin ya daure masa kai. Tun farko ma bai kamata Indiyawan su shigo ba. Tun daga tashar jirgin sama da suka sauka ya kamata a tasa keyarsu komawa inda suka fito.
Duk kokarin jin bahasin hukumar shige da fice ta kasa ya cutura.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum