Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofin Duniya: Najeriya 1 - 0 Bosnia-Herzegovina


Emmanuel Emenike da Najeriya.
Emmanuel Emenike da Najeriya.

Najeriya fa ta kawo karshin rashin nasarar cin wasa a gasar cin kofin duniya...

Najeriya fa ta kawo karshin rashin nasarar cin wasa a gasar cin kofin duniya, a karo na farko a shekaru 16, bayan cinye Bosnia-Herzegovina da ci daya mai ban haushi, sakamakon cin da Peter Odemwingie yayi musu a wa’adin farko na wasa, kuma hakan ya kawo karshen Bosnian, wadanda wannan shine karonsu na farko zuwa gasar.

Najeriya yanzu maki daya kawai take bukata a wasan da zata yi da Argentina domin zuwa zagaye na biyu. Idan ba’a manta ba, Argentina ta rika ta haye zuwa zagayen, inda ta samu nasara akan Iran da ci daya da babu.

Wasan Najeriyan an gudanar dashi ne bayan da Ghana tayi kunnen doki da Jamus, inda suka yi 2-2, kuma nasarar Najeriya ya baiwa mutan nahiyar Afirka abun alfahari da karfin gwiwa, saboda kungiyoyin nahiyar basu yi wani abun arziki ba a wannan gasa. A wasanni 7 da sukayi, Cote’d Voire ce kawai tayi nasara, sannan Najeriya tayi kunnen doki. Yanzu kasashen Afirka sunyi nasara a wasanni biyu, da kuma kunnen doki biyu.

“Wannan abun farin ciki ne ga Afirka”, inji golan Najeriya Vincent Enyeama. “Afirka na bukatar wannan nasara, abunda zai baiwa jama’a karfin gwiwa a gida.”
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00
XS
SM
MD
LG