Amma a wannan gasa dake cike da abubuwan ban mamaki, Brazil dai ta fara shakkar Kamaru, kafin wasan da za’a yi ran Litinin dinnan mai zuwa a birnin Brasilia.
‘Yan wasan Brazil din sunyi ammana cewa yin wasa da kungiyar da bata da wani abun rashi, wahalar wasan zai iya fin yadda ake zato.
“Zamu yi arangama ne da kungiyar da bata da wani abun da zata rasa,”, dawan wasan bayan Brazil David Luiz yace. “’Yan wasansu zasu yi kokarin nuna cewa zasu iya yin wasan da yafi wasanni biyu da suka yi a baya. Cinye mai masaukin baki zai zaman musu kamar cin kofin ne baki daya.”
Brazil dai yanzu itace a saman rukunin group G da maki 4.