Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsokaci Akan Wasannin Kasashen Afirka a Brazil


​Biyo bayan kunnen doki da Najeriya tayi da Iran a gasar cin Kofin Duniya da 0-0, ita kuma kasar Ghana, Amurka ce ta bata kashi.

Mahamadoul Kafi Djibrilla daga Janhuriyar Nijar, mai fashin baki ne akan harkokin wasanni da rubutu, yayi tsokaci.

“Kamaru, kafin su je gasar dama suna da matsalar kudi. To idan zaka je kwallo, kuma hankali bai kwanta ba, dole a samu matsala”, a cewar Mr. Djibrilla.

Game da wasan Ghana kuwa “sun saba cin Amurka, sai sukayi kwallo wanda bai kamata ba, sun saka zuciya, amma basu yi nasara ba. Najeriya kuwa, Iran ya kamata a ce ta ci, amma sai sukayi kunnen doki.”

Mr. Mahamadoul Kafi yace baza’a iya tantance irin tasirin da kungiyoyin kasashen Afirka zasu yi ba, sai Aljeriya ta kammala wasanta da Beljom.
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:12 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG