Cibiyar da ke kare yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya, ta ayyana cutar kyandar biri a matsayin wani al’amari na kiwon lafiya da ke bukatar daukan matakan gaggawa.
Cikin wata sanarwa da ta wallafa shafin yanar gizonta, cibiyar ta ce matsalar ta kyandar biri abin damuwa ne dauba da cewa ta shafi yankin nahiyar Afirka ne.
“Wannan ayyanawa da aka yi na nuni da a dauki matakai na hadin kai cikin gaggawa a tsakanin mambobin kasashen nahiyar don a dakile yaduwar cutar.” Sanarwar ta ce.
A ranar Laraba, Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kiran a hada taron kwararru don daukan matakan gaggawa kan cutar.
Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce an samu fiye da mutum 14,000 da suka kamu da cutar, da kuma mutuwar mutum 524 wadanda tuni suka zarce adadin na bara.
Ya zuwa yanzu dai, fiye da kashi 96% na duk lokuta da mace-mace suna cikin ƙasa guda wato Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo.
Masana kimiyya sun damu da yaduwar sabon nau'in cutar a kasar, wanda zai iya yaduwa cikin sauƙi tsakanin mutane.
Dandalin Mu Tattauna