Sakonsa na wannan shekarar ya karkata ne akan kalubale da kasa take ciki na tabarbarewar tsaro da kuma tashe-tashen hankula.
Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ya kuma yi la'akari da rashin ilimi wanda yace yana cikin daya daga umalubaisan matsalolin kasar.
Ya janyo hankalin shugabanni musamman na yankin arewa akan rata da aka yiwa arewa ta bangaren ilimi. A harkokin ilimi kasar tana baya da sauran kasashen duniya haka kuma arewa na bayan kudancin kasar. Babbar matsalar ita ce 'ya'yan arewa basa zuwa makaranta sai yawo a hanya. Yace ya kamata a tilastawa iyaye su kai 'ya'yansu makaranta. Ya kira gwamnati tayi doka. Duk iyayen da suka hana 'ya'yansu zuwa makaranta a hukuntasu.
Da ya juya akan tashe-tashen hankula a kasar kuma Mai Martaba Sarkin Musulmi yace babu wata hujjar da zata sa 'yan Najeriya su dinga kisan juna saboda banbance banbance dake tsakaninsu. Yace Allah ya yiwo mutane da yare daban daban da addinai daban daban. Da Allah ya ga dama sai ya yi mutane su zama yare guda kawai. Saboda haka ya kira jama'a da a cigaba da zama lafiya da kowanene. A yi hulda da mutane. A daina duba kabila ko addini.
Akan sabbin shugabanni da aka zaba kuwa Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad yace ya zama wajibi a dinga fada masu gaskiya ba tare da tsoro ko fargaba ba. Yace a ji tsoron Allah talakawa da shugabanni. Yace koina a kasar akwai matsaloli. Akwai rashin tsaro, tashin hankalin samari, rashin walwala da rashin abinci.
Ga rahoton Murtala Farul Sanyinna.