Malam Musa Muhammad ya fara da cewa azumi farilla ne ana kuma bukatar kiyayeshi.
Na farko kiyaye azumi shi ne mutum ya kame bakinsa da cin abinci. Na biye dashi shi kame gabanka daga ta'adi. Wadannan biyu su ne suke da saurin karyawa mutum azumi.
Akan neman ladar Ubangiji, Malam Musa yace ana son ka yi sahur kusan gari ya waye. Idan mutum ya yi haka zai samu lada mai tsoka. Idan kuma mutum na son karin lada bayan azumin to da an ce rana ta fadi mutum ya gaggauta ya sha ruwa.
Dangane da sallah lokacin azumi mutum ya tsaftace kansa ya yi alwala. Idan ya shiga masallaci to kada ya riga liman tada kabara. Amma da zara liman ya tada kabbara to shi ya tada tasa to ya samu salla cikakkiya. Haka ma kada a riga liman idar da salla domin a samu cikakkiyar salla mai lada.
Akan zakka Malam Musa yace idan kana da shanu talatin suka shekara daya cur a hannunka do zaka fitar da daya ka bayar zakka idan kana yiwa Allah da manzonsa biyayya. idan basu kai shekara daya ba basu kai zakka ba.
Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal.