A yau Talata Majalisar Dattawa ta fara zamanta na farko bayan dawowa daga hutu, kamar yadda aka saba duk lokacin da Majalisa ta dawo sai shugaban Majalisa ya yi jawabin maraba da kuma karanta wasiku idan akwai.
Bayan kwashe sa’o’i uku ana zaman da yawa daga cikin ‘yan Majalisu suka dauki iznin zuwa sallah, kafin dawowa sai ga sanarwar cewa an sauya shugaban masu rinjaye na Majalisar, Sanata Ali Ndume, inda aka maye gurbinsa da Sanata Ahmed Lawal.
Yanzu haka dai ‘yan Majalisun bas u bayar da wani dalili na tsige shugaban ba, kasancewar suna da hurumin sauya shugabansu ba tare da sun bayar da wata hujja ba.