Wani masanin harkokin tsaro Dakta Kabiru Adamu ya ce janyewar sojojin Chadi na iya haifar da gibi musamman a arewacin jihar Borno da zirin tafkin Chadi. Ya ce “kasancewar su ya inganta tsaro a yankin, toh janyewa da suke yi yanzu ya bar gibi". Ya ci gaba da cewa labaran dake zuwa musu na cewa mazauna kauyukan da aka janye sojojin sun fara barin wurin.
Shi ma Manjo Janar Junaidu Bindawa tsohon babban kwamanda ne na rundunar yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, ya ce abin ban al’ajabi ne da aka janye sojojin kai tsaye. Ya kara da cewa akwai wasu matakai da ya kamata a bi kanfin janye sojojin da yawan su ya kai dubu da ‘yan kai.
Janar Bindawa ya ce kamat ya yi a fara janye jami’an da ba a tsananin bukatar su kafin bayan wani lokaci sai a janye sauran, kuma za a yi hakan ne a wata yarjejeniya tsakanin gwamnatocin Najeriya da Chadi. Amma ficewar da suka yi a daidai wannan lokaci da ya kamata an jinkirta.
Dakta Kabiru Adamu ya ce akwai bukatar daukar matakan gaggawa daga rundunar sojojin Najeriya. Ya ce kungiyoyin Jamā'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihād da reshen kungiyar IS na Afrika ta yamma za su iya amfani da damar janyewar sojojin Chadi su kai hare hare a wadannan wurare, idan sojojin Najeriya basu dauki mataki a cikin dan lokaci ba.
Sashen Hausa na Muryar Amurka ya yi kokarin jin ta bakin sojojin Najeriya, amma ya ci tura, sai dai fadar gwamnatin Najeriya ta bayyana cewar wannan janyewar da sojojin Chadi suka yi babu wata barazanar tsaro da hakan ka iya haifarwa duba da matakan da helkwatar tsaron kasar ke shirin dauka nan bada jimawa ba.
Domin karin bayani saurari rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja:
Facebook Forum