Jami’an sojojin Najeriya na rundunar Operation Lafiya Dole, sun yi yunkurin kwashe mutanen kauyukan Jakana da Minok da ke karamar hukumar Kaga a jihar Borno, sakamakon zargin cewa akwai alaka tsakanin mutanen kauyukan da ‘yan kungiyar Boko Haram.
Sai dai bayan da kwamandan rundunar Lafiya Dole, Olusegun Adeniyi ya gana da gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya umarci janye wannan yunkuri na sojojin.
Gwamnan jihar Borno ya bayyana cewa basa goyon bayan tayar da mutanen daga kauyukan su, amma suna goyon bayan sojojin su yi bincike domin zakulo duk wadanda ke fakewa suna aikata laifi.
A kwanan nan dai sojojin Najeriya na fuskantar hare-hare daga mayakan kungiyar Boko Haram, wanda hakan ya sa suke zargin ‘yan bindigar na fitowa ne daga wadannan kauyuka suna far musu.
Tun da safiyar ranar Talata ne aka datse hanyoyin garin Maiduguri zuwa Damaturu, inda jami’an sojin suka yi ta shiga kauyukan da manyan motoci da nufin kwashe mazauna kauyukan.
A cewar wasu mazauna kauyukan da Muryar Amurka ta zanta da su, sojojin sun tara su guri guda, suka kuma kirga su tare da sanar da su zasu kwashe su domin akwai ‘yan Boko Haram a cikinsu. Sai dai da aka tambayesu ko an taba kama wani ‘dan Boko Haram a kauyukan? Sun ce ba a taba ba.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Haruna Dauda.
Facebook Forum