Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Yi wa Ma’aikatan NNPC Da Sojojin Najeriya Kwanton Bauna


Dakarun Najeriya a lokacin da suke tafiya a kan wata hanya da ke jihar Adamawa a ranar 26 ga watan Maris din 2016
Dakarun Najeriya a lokacin da suke tafiya a kan wata hanya da ke jihar Adamawa a ranar 26 ga watan Maris din 2016

Rahotanni daga Maiduguri da ke Jihar Bornon Najeriya na cewa an yi nasarar kubutar da ma’aikatan matatar man fetur din kasar na NNPC bayan da wasu da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka yi masu kwanton-bauna tare da sojojin Najeriya da ke masu rakiya a kan hanyar Magumeri da Gubio.

Bayanai na ci gaba da bayyana kan yadda wasu da ake tunanin ‘yan Boko Haram ne suka kai hari akan ayarin motocin ma’aikatan matatar man fetur din Najeriya ta NNPC da sojoji da ke masu rakiya yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani yanki da ake aikin neman man fetur a jihar Borno.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto an samu tabbacin mutuwar sojoji takwas da wani dan Civilian JTF guda da ke taimakawa jami’an tsaro wajen yaki da masu ta da kayar baya a cewar wata sanarwa da dakarun Najeriya suka fitar.

Sai dai wata majiya daga asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri ta fadwa Muryar Amurka cewa adadin wadanda suka mutu yana da yawa.

“An kawo mutane cike da Hilux-Hilux, motocin za su kai biyar kuma duk gawarwaki ne a ciki wallahi.” In ji majiyar asibitin.

Wani dan uwan dan Civilian JTF da ya samu kubuta daga harin bayan da aka harbe shi a ka ya ce ‘yan Boko Haram ne suka bude masu wuta.

“Suna cikin tafiya ne kawai sai Boko Haram suka bude masu wuta, akalla sun tafi da mota ta kai 12 an harbi ‘yan Civilian JTF biyar, shi kanina Allah ne ya ba shi ikon guduwa inda ya yi tafiyar tsawon kilomita tsakanin 10-20 kafin ya kawo bakin titi inda abokanan aikinsa da suka kawo dauki su dauke shi.” In ji Dahiru Alhaji Abubakar, wanda ke jinyar kaninsa dan civilian JTF a asibiti.

Harin ya auku ne a ranar Talata a lokacin da ayarin motocin wasu ma’aikatan matatar man ta NNPC ta Najeriya ke kan hanyarsu ta zuwa wani yanki da ake aikin neman man fetur.

Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Maiduguri, Haruna Dauda Biu ya ce jami’ar Maiduguri ta tabbatar wa manema labarai cewa akwai malamanta guda tara a cikin wadanda wannan lamari ya rutsa da su.

Wasu majiyoyi sun ce ma’aikatan na NNPC malaman jami’ar Maiduguri ne da ke koyarwa a sashen ilimin hakar ma’adinan karkashin kasa, wadanda NNPC ta diba a matsayin ma’aikatan kwantiragi domin gudanar da aikin.

Ko da yake, wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya Brigadier Sani Usman Kuka-sheka ya fitar, ba ta danganta ma’aikatan da jami’ar ta Maiduguri ba, inda kawai ta ce an kubutar da ma’aikatan NNPC.

Sanarwar har ila yau ta bayyana cewa sojojin Najeriyar sun yi nasarar sake kwato motoci guda hudu da manyan makamai da suka hada da bindigar kakkabo jiragen sama da motocin NNPC da kuma motar Civilian JTF da harsashai da dama.

Sai dai rundunar sojin Najeriya ba ta ambaci ko an kama wasu daga cikin mayakan na Boko Haram ba.

Wannan hari na zuwa ne kasa mako guda bayan da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Burtai ya ba da wa'adin kwana 40 da a kamo shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau a raye ko mace.

Saurari rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG