A yau dai ana sayar Dalar Amurka akan Naira 485 zuwa sama, sabanin ‘kasa da haka da aka sayar da ita a watannin baya. Hakan dai na faruwa ne duk da cewa ‘yan Najeriya da yawa dake tururuwar komawa gida domin gudanar da bikin Krisimeti.
A kokarin da gwamnatin Najeriya keyi na samarwa da Naira karfi a tsakanin kudaden kasashen ketare, ko a kwanan baya sai da gwamnati ta fara daukar matakai na kama masu hada-hadar kudaden kasashen ketare wanda ake zargi da sayar da takardar kudin Dalar Amurka a kudin da ya haura na hukuma.
Cikin wannan makon ne dai aka zabi gwamnan bankin Najeriya
Godwin Emefele, a matsayin shugaban wata hukuma ta bankin Islama, wadda ta hada wasu kasashe tara da bankin Islama, da zummar gudanar da harkokin kudi da musayar kudade a tsakanin kasashen bisa tsari irin na Islama.
Kasashen da suka hada wannan kungiyar dai sun hada da kasar Kuwait da Luxembourg da Malesia da Mauritius da Najeriya da Qatar da Turkiyya da hadaddiyar daular larabawa da kuma bankin Islama.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.