Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hedkwatar Rundunar Sojojin Najeriya Ta Musanta Korafin da Wani Soja Yayi a Faifan Bidiyo


Hafsan Rundunar Sojojin najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai
Hafsan Rundunar Sojojin najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai

Makon jiya ne wani soji da ba'a tantance ba ya dinga korafi akan wuyar da suke sha a dajin Sambisa inda iska da ruwan sama ke damunsu amma kuma hedkwtar sojojin tace mai korafin sojan gona ne domin babu wanda ya sanshi

Daraktan labarai na hedkwatar rundunar sojojin Najeriya Manjo Janar John Eneche ya shaidawa Muryar Amurka cewa ya ga bidiyon inda sojan da ba'a tantance ba yake korfe korafe akan halin da wai sojoji suke ciki a dajin Sambisa.

Janar Eneche yace yayi yaki a dajin Sambisan. Yace sojan yayi korafin cewa ruwan sama ya lalata masu inda suke fakewa. Yace to amma a aikinsu na soja akwai abubuwan da mutum bashi da iko a kansu. Ruwan sama na cikinsu kuma yana faruwa a koina. Yace a wurin soja wannan ba hanzari ba ne.

Yace ko hafsan sojojin shi kansa yana kaiwa yana kawowa cikin dajin Sambisan. Batun iska ko ruwa ya lalata masu wurin fakewa ba batu ba ne. Yace a matsayin mutum na kasancewa soja da wuya ka gamsu da kowane wuri.

Dangane da sojan da ya dinga korafi Manjo Janar Eneche yace shi sojan an tantanceshi? Yace yana da kyau a yi takatsantsan saboda irin kafofin Facebook kafofi ne na farfaganda kawai. Yace ba'a raba sojan da zama sojan gona ba.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yaki Da Matsalar Almajiranci A Nasarawa
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG