Sabon mai koyar da Accra Hearts of Oak wasa, samuel Boadu ya nace kan cewar a shirye ya ke ya yi aiki tsakaninsa da Allah yayin da dai ya soma kama aiki da Phobia.
Boadu dai ya yi wannan alkawari ne yayin da ake kaddamar da shi a ranar Litini, inda ya kulla yarjejjeniyar shekara uku da rabi. "Ina son in yi anfani da wannan dama in gode wa shugaba na hukumar diraktocin Hearts Of Oak da ya bani wannan damar, in bayar da gudunmuwa ta a cikin wannan iyali," inji shi.
Tsohon mai tsaron gida na Black Stars, Daniel Adjei ya kulla wata yarjejjeniya na gajeren lokaci da wani babban kulob din kasar Habasha, Wolaita Dicha FC. Dan wasan mai shekaru 31 ya rataba hannu akan wata kwangila da kulob din dake da matsuguni a Sodo har karshen kakar shekarar ta dubu biyu da ishirin da daya , Adjei dai na tare da Makelle kenema saboda dalilin yakin Trigray kulob din ba ta taka leda a cikin Firimiya Lik din Habasha a wanna kakar wasa ta bana.
'Yan sanda sun kama wani dan wasan baya na Aduana FC a bisa zargin da ake masa na buge wani dan sanda da motarsa, inda ya mutu har lahira. Adams Farouk an kame shi ne a a Ahinkrom bayan ya buge jamin 'yan sandan da motar tasa. Dan wasan yanzu haka ya na hannun 'yan sanda kuma an caje shi da buge mutum da mota ya kuma arce. Wannan hadari dai ya faru ne a Soshianu...kan hanyan Brekum.
Da karfi da yaji aka matsanta wa tsohon a wasan Chelsea kuma dan wasan kasar Ghana, Micheal Essien ya share goyon bayan da yake nuna wa masu ra'ayin madigo da kuma luwadi a kasar Ghana.
Tsohon dan wasan na AC Milan da Real Madrid dai ya sha suka da caccaka bayan da ya fito fili yana nuna goyon bayansa ga wannan al'amari a kasar. Gabanin dai haka sai da wadansu shahararrun mutane a fadin duniya da suka hada da Idris Alba da Naomi Campbell suka hade da wasu taurarin guda sittin da bakwai su ka bayyana goyon bayansu ga wannan dabi'a a Ghana. Essien dai ya ga ba shi da zabi illa ya goge ra'ayin nasa akan twitter.
Ga cikakken labarin wasannin a cikin sauti, wanda Ridwanullah Abbas, ya hada.