A Lokacin da nake jihar Lagos ina gabatar da barkwanci a gaban mutane wanda a turance ake cewa stand-up comedy amma tun da na dawo Arewa sai harkata ta tsaya sakamakon rashin karbar wannan salo da ake yi a Kudu a Arewacin Nijeriya, inji sarkin barkwanci Nuradeen Ado Mai Wuka, wanda akafi sani da WHY malam.
WHY malam ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da Wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir a Kano, yayin da suke hira akan wannan sana’a tasa.
Ya ce lokacin da ya dawo Arewacin kasar nan ya yi kokarin kwatanta barkwanci kamar yadda yake yi a jihar Lagos, hakan bai yi wu ba sakamakon rashin daukar nauyi daga masu ruwa da tsaki kamar yadda ake yi a Kudancin kasar.
WHY Malam, ya kara da cewa a can Kudu, kamfanoni da daidaikun mutane na marawa masu harkar nishadi baya don inganta fannin sabanin haka a nan Arewacin Nijeriya, wanda hakan na dakile tare da karya gwiwar masu irin wannan sana’a.
Matashin na harkar nishadi ne da ta danganci fannin waka, inda yake jagorantar mawaka a wuraren biki ko suna ko wani taro tare da baiwa mutane dariya a lokacin taro.
Daga karshe ya ce burinsa Alla ya kawo lokacin d za’a dinga nuna shi’awar irin wadannan wasannin barkwanci a manyan gidajen talabijin da ke kan satellite wanda zai bashi dama ya rika jagorantar manyan mawakan duniya irinsu 50 cents da makamantansu.
WHY malam ya ce baya waka amma yana mu’amala da mawaka sanadiyar yawan barkwancinsa da kuma kokarinsa na nishadantarwa.
Facebook Forum