Masu sha’awar wasanni a fadin duniya sun rasa kalmomin da za su yi amfani da su wajen bayyana yadda suke ji danga
Masu sha’awar wasanni a fadin duniya sun rasa kalmomin da za su yi amfani da su wajen bayyana yadda suke ji dangane da labarin mutuwar shahararren tsohon dan wasan kwallon Kwando na Amurka, Kobe Bryant, wanda ya zo masu kwatsam..
Bryant da ‘yarsa 'yar shekaru goma 13 da haihuwa su na cikin mutune tara da suka mutu jiya Lahadi a wani hadarin jirgin mai saukar ungulu a wajen birnin Los Angeles.
Rahotannin sun ce su na kan hanyarsu ne ta zuwa kallon wata gasar kwallon Kwando da aka shiryawa matasa.
Da ma Bryant ya saba amfani da jirgi mai saukar ungulu zuwa wurin kallon wasa daga gidansa a Los Angeles don kaucewa cunkoson mototci a cikin birnin.
Rundunar 'yan sandan Los Angeles ta ce ta na ci gaba da gudanar da binciki a kan musabbabin hadarin tare da taimakon jami'an gwamnatin tarayya, amma har yanzu ba su fitar da wasu bayanai akan abin da ya haddasa hadarin ba, ciki har da ko yanayin hazon jiya Lahadi da safe ya taka rawa a faruwar hadarin ko a'a.
A halin da ake ciki, hukumomi sun yi kira ga jama'ar yankin da jirgin ya fada a ciki da su kaucewa kusantar wurin.
Alex Villanueva wanda shi ne shugaban 'yan sandan birnin Los Angeles, ya ce, "zuwa wurin da jirgin ya fadi na da wahala, amma a yanzu su na fuskantar matsalar dandazon jama'a masu jimami, ya kamata jama’a su kaucewa wannan yanki."
Facebook Forum