Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 129 Sun Mutu A Yunkurin Tserewa Daga Gidan Yarin Congo


Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta ce akalla mutum 129 ne aka kashe a lokacin da suke kokarin tserewa daga gidan yarin na Makala da ke Kinshasa babban birnin kasar da yammacin ranar Lahadi.

Hukumomin kasar sun ce an shawo kan lamarin ya zuwa yanzu.

A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X da safiyar ranar Talata, ministan harkokin cikin gida Shabani Lukoo ya ce gobara ta kuma tashi a ginin gidan yarin da rumbun adana abinci da kuma wani asibiti. Ya kara da cewa wasu mutane 59 ne sun jikkata.

Mutum 129 Sun Mutu A Yunkurin Tserewa Daga Gidan Yarin Congo
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:10 0:00

"Yukurin tserewa da aka yi a gidan yarin tsakiyar Makala ya haifar da asarar rayuka da kuma barna mai yawa." Sanarwar faifan bidiyon ta ce.

Tun da farko wani jami’in gidan yarin ya ce babu wani fursuna da ya yi nasarar tserewa, ya kara da cewa an kuma kashe duk wadanda suka yi yunkurin tserewa. Gwamnati na binciken lamarin.

Yunkurin ballewar ya faru ne da misalin karfe 2:00 na safe (0100 GMT) ranar Lahadi.

Fursunonin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun dai ji karar harbe-harbe, da kuma karar fursunoni a waje.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG